News
Tarayyar Turai ta sanya takunkumi kan mutanen da ke da hannu a rikicin gabashin Kongo
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tarayyar Turai ta sanya takunkumi kan mutanen da ke da hannu a tayar da rikice-rikice gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo.
Wadanda aka sanya wa takunkumin sun hada da mai magana da yawun ‘yan tawayen M23, Willy Ngoma, an zargi kungiyar da hannu a matsalar tsaro da ta ɗabaibaye ƙasar da kuma keta ‘yancin dan adam da kuma cin zarafi.
Majalisar Dinkin Duniya ma ta zargi kungiyar da kashe mutum sama da 130 a mako da ya gabata, abu kuma da ‘yan tawayen suka musanta.
Tarayyar Turai din ta kuma kakaba wa wani baban sojan ƙasar ta Kongo, Joseph Nganzo Olikwa takunkumi kan tafiye-tafye da kuma toshe asusun sa na banki bayan da aka zargi dakaru da ke karakshinsa da kai hare-hare da yin fyade.
Advertisements
