Politics
ba zan janyewa wani dan takara ba domin marawa kowane dan takara baya ba-Salihu Tanko Yakasai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar PRP Hon. Salihu Tanko Yakasai ya ce ba zai janyewa kowanne dan takara ba kafin da kuma bayan zaben 2023.
Salihu Tanko Yakasai ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga dan takarar gwamnan jihar ADP Hon. Sha’aban Sharada OON yana kira ga sauran ‘yan takarar gwamna da su janye masa.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Kakakin dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP Suhaib Auwal Gwagwarwa ya ce, Hon. Salihu Tanko Yakasai ba zai janye takararsa domin marawa kowane dan takara baya ba, ya kara da cewa a shirye suke su shiga zaben dan suman nasara.
Ya kara da cewa, Salihu Tanko Yakasai dan takara ne mai zaman kansa, mai neman ci gaban jihar Kano, ba ya yiwa kowa aiki, kuma ba wani ne ke daukar nauyinsa ba.
“Idan Sha’aban Sharada yana ganin ya fi kowane dan takara cancanta, da ya nemi ‘yan takarar APC da PDP su janye masa takara, domin su ‘yan takara ne ba mu ba”.
Salihu Tanko Yakasai ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su yi amfani da hankalinsu wajen zaben gwamna na gaba kuma su zabi shugaban da ya cancanta da zai farfado da Kano a zamaninta da kuma daukaka martabar jihar Kano don yin tattaki a sauran manyan biranen duniya.
