News
INEC ta gargaɗi masu son sayen ƙuri’u a zaɓukan Najeriya na 2023
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ja kunnen ƴan ƙsar da su guji saye da sayar da ƙuri’a a yayin zaɓukan da ke tafe a farkon shekarar 2023.
Jaridar Daily Post ta intanet da ta ruwaito INEC a yau, ta ce duk wanda aka kama da laifin zai fuskanci ɗaurin shekara guda a gidan yari da kuma biyan tarar naira 500,000.
Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan koke-koken da jama’a suka yi na zargin cewa ƴan siyasa na son sayen ƙuri’u a zaɓukan da ke tafe.
INEC na cikin matsin lambar ganin ta gudanar da sahihin zaɓe marar maguɗi da hana sayen ƙuri’un mutane – wanda yana cikin dalilan da suka sa babban bankin ƙsar ya ce ya ɗauki matakin sauya kuɗaden naira da rage yaɗuwar sabbin kudin don hana wannan ta’asa.
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
