Connect with us

News

Na yi wa ‘yan Najeriya duk abin da zan iya – Shugaba Buhari

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan kasar da su shiga sabuwar shekarar 2023 da fatan ganin kasar ta ci gaba da fuskar hadin kai da fatan ci gaba.

 

Advertisement

Cikin sakon sa na sabuwar shekara da ya aika a jiya, Shugaba Buhari ya ce 2023 shekara ce da za a kara mayar da hankali kan harkokin tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yakin da cin hanci.

Muhimman abubuwan da suka faru a shekarar 2022

Buhari wanda ya yi maraba da suka da yabon da ‘yan Najeriya ke yi masa, ya ce ya yi iya abin da zai iya ga mutanen kasar, yayin da yake fatan duk shugaban da zai zo ya dora daga inda ya tsaya, domin ciyar da Najeriya caga.

 

Ya ce dole yan Najeriya su dauki ragamar tabbatar da zabukan da za a yi a 2023 an yi su babu cuta babu cutarwa.

 

Ya kuma shawarci ‘yan kasar da su kiyaye da tayar da hankali a lokutan zabe, su kuma kiyaye daga duk wani dan siyasa da zai nemi s u yi hakan.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending