News
Mutum huɗu sun rasu sakamakon karon da jiragen sama suka yi a iska
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Mutum huɗu sun rasu bayan wasu jirage masu saukar ungulu biyu sun yi karo a saman iska kusa da tekun Australiya.
Ƴan sanda a Jihar Queensland ta Australiya sun ce binciken farko wanda aka soma ya nuna cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da ɗaya daga cikin jiragen kea tashi wani kuma yana ƙoƙarin sauka.
Shin da gaske sabbin kuɗin Najeriya na komawa farar takarda idan an wanke su?
Waɗanda suka rasu suna cikin jirigin na helikwafta ɗaya. Akwai wasu fasinjoji da ke cikin halin rai kwakwai mutu-kwakwai.
Mutum biyar cikin shidan da ke cikin jirgin waɗanda suka yi saukar gaggawa sun ɗan ji rauni ne.
Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta Austrailiya ta ce tana bincike kan karon da jiragen suka yi.
Advertisements
