Connect with us

News

An Rufe Gidajen Mai 14 A Kano Saboda Sayarwa A Farashin Da Ya Wuce Hankali

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) reshen Jihar Kano, ta rufe gidajen mai 14 bayan da ta kama su suna sayar da man a kan farashin da ya wuce kima.

Advertisement

 

Da yake yi wa manema labarai karin haske game da sintirin da suka yi ranar Alhamis, Jami’in hukumar a Kano, Aliyu Muhammad Sama, ya ce duk da dai a yanzu babu tsayayyen farashin fetur din a hukumance, amma gidajen man kan sayar da shi a farashin da ya wuce misali.

Advertisement

Mutum Miliyan 7 Ne Suka Yi Umarah A 2022 – Saudiyya

 

A cewarsa rufe gidajen man ya zama wajibi bayan da aka gano suna sayar da fetur tsakanin N290 zuwa N300 kan kowace lita.

Advertisement

 

Ya kara da cewa, a watan Disamban bara, hukumar ta rufe gidajen mai sama da 100 na ‘yan kasuwa saboda sayar da shi sama da farashin da hankali zai iya dauka.

Advertisement

 

 

Advertisement

Aminiya ta rawaito cewa Ya ce hukuncin wadanda lamarin ya shafa shi ne tarar N150,000 kan kowane famfo, sannan gidan man zai ci gaba da zama a rufe zuwa lokacin da ya amince ya sayar da fetur din a kan farashin da ya dace.

 

Advertisement

“Ba mu kai ga gurfanar da ‘yan kasuwar da lamarin ya shafa a gaban kotu ba saboda hakan shi ne matakin karshe.

 

Advertisement

“Mun dai dora musu tarar N150,000 kan kowane kan famfo, idan suka ki biya daga nan za mu dauki mataki na gaba.

 

Advertisement

“Za mu ci gaba da farautar gidajen man da ke sayar da fetur din a kan farashin da ya wuce kima,” inji Jami’in na NMDPRA.

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending