Connect with us

News

Kifewar kwale-kwale: An sake gano gawar mutum biyar a Jihar Kebbi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

A watan Mayun 2021 ma jirgi ya kife da mutum kusan 100Image caption: A watan Mayun 2021 ma jirgi ya kife da mutum kusan 100

Advertisement

An gano ƙarin gawar mutum biyar da suka rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi ranar Talata, inda masu aikin ceto ke ci gaba da lalubo sauran.

Likitoci dubu 54 ne kacal suka rage a Najeriya – Ƙungiyar Likitoci

Jirgin ruwan ya kife a garin Samanaji na Karamar Hukumar Koko-Bese lokacin da yake ɗauke da fasinjoji fiye da 100, amma an samu nasarar ceto mafi yawa daga cikinsu.

Advertisement

 

Alhaji Yahaya Bello Koko, wanda shi ne shugaban Karamar Hukumar Koko-Besi, ya tabbatar wa BBC cewa hadarin ya faru ne lokacin da mutanen ke komawa gida daga gona.

Advertisement

 

Ya ce mutane sun cika jirgin maƙil tare da mata da kuma yara, abin da ya sa ya rabe biyu a tsakiyar ruwa kasancewar tsohon jirgi ne.

Advertisement

 

Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa an ceto mutum fiye da 80, inda aka gano gawa 10 a ranar Laraba.

Advertisement

 

Zuwa yanzu an gano jimillar gawa 15 kenan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending