Connect with us

News

Likitoci dubu 54 ne kacal suka rage a Najeriya – Ƙungiyar Likitoci

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ƙungiyar Likitocin Najeriya, NMA ta ce a yanzu haka likitoci dubu 54 ne kacal suka rage domin kula da lafiyar ƴan ƙasar fiye da miliyan 218.

 

Advertisement

Ƙungiyar ta NMA ta ƙara da cewa daga cikin likitocin dubu 54, dubu 18 ne kawai ƙwararru da ke cikin aikin duk da cewa wasu daga cikin dubu 18 ɗin tuni su ma sun bar kasar.

Yadda Mawuyacin Halin Da ‘Yan Gudun Hijira Ke Ciki A Najeriya Yake Shafar Lafiyarsu

A shekarar da ta gabata ne dai fiye da likitocin 2000 suka bar Najeriya zuwa kasashen Turai.

Advertisement

 

Akwai fargabar cewa fiye da likitocin 4000 ka iya barin kasar a sabuwar shekarar nan ta 2023.

Advertisement

 

Da alama kuma yankin arewa ya fi fama da karancin likitoci bisa alkaluman da kungiyar likitocin ta Najeriya ta fitar.

Advertisement

 

Alkaluman dai na nuna cewa yanzu haka akwai likitoci 425 kacal da ke aiki a kafatanin yankin arewa maso yammaci da ke kunshe da mutane kimanin miliyan 50, kusan kaso daya bisa hudu na yawan jama’ar Najeriya.

Advertisement

 

A watan Yuli, alkaluman kungiyar likitocin ta Najeriya sun sake nuna cewa kimanin likitoci 200 ‘yan asalin kasar sun samu lasisin zama likitoci a Burtaniya.

Advertisement

 

Wani rahoto a Mujallar British Medical Journal a 2020 ya nuna cewa da ma akwai karancin likitoci miliyan 2.8 a fadin duniya kuma matsalar ta fi shafar kasashe masu tasowa irin su Najeriya.

Advertisement

 

Yanzu tambayar da jama’a da dama ke yi ita ce shin adalci ne ace manyan kasashen duniya su rinka kwashe likitocin ƙananan kasashen da dama tsarin lafiyarsu ke cikin wani hali?

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending