News
Dakarun Rasha sun kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi a garin Sevastopol na Ukraine
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dakarun da ke biyayya ga ƙasar Rasha a Ukraine sun ce sun kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi da aka yi niyyar kai musu hari da shi a sansaninsu da ke garin Sevastopol.
Zuwa yanzu hukumomin Ukraine ba su tabbatar da kai harin ba, amma hakan na nufin ba a mutunta tsagaita wutar da Shugaba Putin na Rasha ya ayyana ba saboda Kirsimetin ‘yan gargajiyar Kiristoci ba.
BBC ta rawaito cewa an samu rahotannin kai hare-haren atilare tsakanin ɓangarorin biyu a yankin Donetsk.
Shugaba Putin ya aika saƙon Kirsimetin, yana mai cewa ranar “ta jawo aikata ayyuka na gari da kuma burika”.
Advertisements
