News
Likitoci NARD suna barazanar shiga yajin aiki a kasar nan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar likitocin Najeriya NARD ta yi barazanar shiga yajin aikin gama gari idan gwamnatin tarayya ta ki biya mata bukatunta.
Yan sanda sun kama mace mai safarar makamai
Kungiyar a cikin wata wasika da ta aikewa Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, mai dauke da sa hannun shugabanta, Dokta Emeka Innocent Orji, ta ce za a fara gudanar da yajin aikin ne idan ba a magance matsalolin ba a gaban majalisar zartarwa ta kasa ta Janairu 2023 (NEC) taron da aka shirya gudanarwa tsakanin 24 zuwa 28 ga Janairu.
Sanarwar ta cigaba da cewa gwamnati tana ruke hakkin likitocin kasarnan duk da kuwa irin aikace aikace da likitocin keyi
Advertisements
