News
Yan sanda sun kama mace mai safarar makamai
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar kama wasu mutum biyu masu safarar makamai zuwa jihar ciki har da mace guda.
Mutanen biyu – masu suna Emmanuel Emmanuel da wata mace mai suna Nana Ibrahim an kama su ne a kan hanyar Gusau zuwa Wanke zuwa Dansadau – an kama su ne dauke da harsasan bindiga kimanin 325, da mazubin harsasai na ƙirar bindigar AK47 guda ɗaya.
Sanarwar ta ce an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan mutanen wadanda ake zargin sun ɗaukpo makaman ne daga jihar Benue zuwa wani sansanin ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Rundunar ta ce a yayin tuhumarsu mutanen sun amsa laifin cewa sun dade suna gudanar da wannan haramtaccen kasuwanci tsakaninsu da ‘yan fashi a Zamfara da wasu jihohi makwabta.
Kwamishin ‘yan sandan jihar Kolo Yusuf ya jaddada burin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kiran jama’a da su hada hannu da hukumomin tsaro domin tabbatar da ƙudurin rundunar.
A ƙarshen makon da ya gabata ma dai rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarar ƙwace makamai masu yawa a jihar daga hannun masu safarar makaman waɗanda rundunar ta ce sun ɗauko makaman ne daga jihar Taraba domin kai su sansanin ‘yan fashin daji.
