News
ƘAUYE MAFI DOGON SUNA A DUNIYA
ƘAUYE MAFI DOGON SUNA A DUNIYA
Wani tudu ne kusa da Porangahau, kudu da Waipukurau a kudancin Hawke’s Bay, a ƙasar New Zealand. Tsayin tudun ya na da mita 305 (1,001 ft). Ƙauyen ya shahara da farko saboda dogon sunansa wanda ba a saba gani ba, wanda ya fito daga Māori; Sau da yawa ana rage shi zuwa Taumata don taƙaitawa.
Ya sami ma’auni na daraja kamar yadda shi ne sunan wuri mafi tsawo da aka samu a kowace ƙasa mai magana da harshen Ingilishi, kuma mai yiwuwa sunan wuri mafi tsawo a duniya, a cewar ‘World Atlas.’
An kuma jera sunan tudun (mai haruffa 85) a cikin ‘Guinness World Records’ a matsayin sunan wuri mafi tsawo.
Taumatawhakatangihangakoauauotamateaturipukakapikimaungahoronukupokaiwhenuakitanatahu.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
