News
Masu Sana’ar POS A Kano Sun Koma Zaman Tagumi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Masu sana, ar POS a jihar Kano a kwana biyun da suka gabata, sun tsinci kan su a wani matuwacin hali na fama da rashin kuɗi a hannu.
Yanzu haka dai da dama cikin Masu sana,ar POS na ci gaba da kokawa kan yadda kudin ke wahalar samuwa a bankuna.
Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Bayan Karin Wa’adin Canjin Kudi
Jaridar indaranka ta rawaito cewa yanzu haka masu POS suma basu da kudin da zasu dinga gudanar da sana’ar ta su.
Wani mai sana’ar POS Dahiru Abdullahi mazaunin unguwar uku ya ce suma bankuna idan sun je basa samun damar daukar kudin, ko da kuwa sun shiga cikin bankin da sunan su samu sababbi.
Yanzu haka dai bakin ATM dogon layi kuma kudi kadan yake bayarwa, yayin da masu POS suka koma tagumi.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
