Connect with us

Sports

Yau ake kulle kasuwannin musayar ‘yan wasan Turai ta bana

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kammala cinikayyar ‘yan wasan na nuna cewa za a koma wasanni gadan-gadan musamman wasannin gasar cin kofin zakarun Turai.

 

Advertisement

 

Yau talata ake rufe kasuwar musayar ‘yan wasan kwallon kafa ta wannan kaka, inda Firimiyar Ingila ke kulle kasuwarta da misalin karfe 23:00 agogon GMT dai dai lokacin da bayanai ke nuna yiwuwar kudin da kungiyoyi suka kashe wajen cinikayyar ‘yan wasan a bana ta iya zarta kowanne lokaci a tarihi.

Advertisement

 

Masu Sana’ar POS A Kano Sun Koma Zaman Tagumi

Ya zuwa yanzu alkaluman. da aka tattara sun nuna yadda aka kashe tsabar kudin da yawansu ya kai fam miliyan 550 a wannan wata, wanda ya karya tarihin adadin fam miliyan 430 da kungiyoyin suka kashe a kakar wasa ta shekarar 2018.

Advertisement

 

Firimiyar Ingila za ta kulle kasuwar da misalin karfe 11 yayinda Scotland ke shirin kullewa a da misalin karfe 23:59.

Advertisement

 

Bayanai sun ce za a rufe kasuwar Bundesliga ta Jamus da karfe 17:00 sai Serie A ta Italiya da za a kulle da misalin karfe 19:00.

Advertisement

 

La Ligar Spain za ta kulle ta ta kasuwar da misalin karfe 23:00 yayinda Ligue 1 ta Faransa za ta kulle kasuwar ta da misalin karfe 11:59 duk dai a yau talata 31 ga watan Janairu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending