Connect with us

Sports

Real Madrid Za Ta Gwabza Da Barcelona A Wasan kusa da Karshe 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Barcelona da Real Madrid za su gwabza a wasan da zai kai daya daga cikinsu zuwa karawar karshe a Copa del Rey na kakar nan.

 

Advertisement

A jadawalin da aka raba ranar Litinin a wasan daf da karshe, Barcelona za ta kece raini da Real Madrid, yayin da Bilbao da Osasuna za su yi karon batta a daya bangaren..

Bankuna za su karbi tsoffin takardun kudi na naira bayan wa’adin ya cika, in ji Emefiele

 

Advertisement

A makonnin da suka gabata ne, Barcelona ta lashe Spanish Super Cup bayan ta doke Real Madrid da ci 3-1 a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

 

Advertisement

Karawar ta hamayya ta El Clasico za a yi ne gida da waje a Copa del Rey, inda Real za ta fara karbar bakuncin wasan farko ranar 27 ga Fabrairu, sai wasa na biyu ranar 3 ga Afirilu a Nou Camp.

 

Advertisement

A cikin watan Oktoba, Real ta doke Barca 3-1 a La Liga, sai dai kuma kungiyar Nou Camp ta bai wa ta Santiago Bernabeu tazarar maki biyar.

 

Advertisement

Kamar yadda jadawalin ya nuna, Osasuna ce za ta fara karbar bakuncin wasan farko, sannan ta ziyarci Athletic a karawa ta biyu.

 

Advertisement

Za a buga wasan karshe a Copa del Rey a filin Estadio de la Cartuja da ke birnin Sevilla a ranar 6 ga watan Mayu.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending