Sports
Harry Kane ya zama ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallo a Tottenham
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ingila Harry Kane ya zama ɗan wasan da ya fi ci wa ƙungiyar Tottenham ƙwallaye a tarihi bayan da ya ci wa ƙungiyar ƙwallo ta 267 a duka gasanni, kuma ta 200 a gasar Premier League.
Kane mai shekara 29 ya yi wannan bajinta ne bayan da ya ci ƙwallo a ƙarawar da ƙungiyarsa ta yi da Manchester City a gasar Premeir ranar Lahadi.
Real Madrid Ta Barar Da Damar Matse Wa Barcelona Lamba A La Liga
A baya Jimmy Greaves ne ke riƙe da kambin wanda ya fi ci wa Tottenham ƙwallaye, inda ya ci mata ƙwallo 266 a wasa 379 da ya buga mata tsakanin shekarar 1961 zuwa 1970.
Kane wanda ya fara buga wa ƙungiyar wasa a shekarar 2011, ya yi wa Tottenham wasa 415 a duka karawa, inda ya buga mata wasannin Premier 304.
