Connect with us

Sports

Wainar Da Aka Toya A Makon Farko Na Firimiyar Ingila Ta Bana

Published

on

DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Crystal Palace da Arsenal suka bude taro da wasan makon farko na gasar Firimiyar Ingila ta bana da ta kankama gadan-gadan.

Arsenal wadda ta taba lashe gasar sau 13 a tarihi, ta yi nasara a wasanta na farko inda ta lallasa Crystal Palace da ci biyu da nema.

Advertisement

Wasa na biyu da aka buga a wasannin makon farko na gasar shi ne wanda Fulham ta karbi bakuncin Liverpool a Craven Cottage da aka tashi canjaras 2-2.

Advertisement

Bournemouth ta yi kokarin kare mutuncin gidanta yayin da ta lallasa Aston Villa a wasansu na ranar Asabar da aka tashi 2-0.

Nottingham Forest ta yi rashin nasara a bakuntar da ta kai wa Newcastle United a St. James Park, inda aka tashi wasan biyu babu ko daya.

Advertisement

 

An hallaka kasurgumin ɗan fashin daji da ya addabi yankunan arewacin Najeriya

Advertisement

Rubdugun kwallaye 4-1 gami da babu sani babu sabo Tottenham United ta nuna wa Southampton a haduwar da suka yi ranar Asabar, lamarin da ya sa kungiyar ta Arewacin Landa ta yi dere-dere a samn teburin Firimiyar Ingila ta maki uku, inda ta yi wa kowacce kungiya fintikau da yawan kwallaye.

Wolves ta kwashi kashinta a hannu yayin da ta je bakunta gidan Leeds United wadda ta zuba mata kwallaye 2-1 a filin wasan na Ellan Road.

Advertisement

Ana iya cewa da kyar Chelsea ta samu maki uku da ci daya mai ban haushi a wasanta da Everton yayin ziyarar da ta je Goodison Park.

Karfi ne ya zo daya a wasan da aka tashi 2-2 tsakanin kungiyar Leicester City da Brentford a filin wasa na King Power.

Advertisement

Lamarin Manchester United dai kusan jiya-i-yau, domin kuwa ba ta wani sauya zani ba kamar yadda ta kasance a kakar wasannin da ta shude.

United dai ta sha kashi a hannun Brighton da ci 2-1 a Old Trafford a wasan farko da ta fara na Firimiyar Ingila ta bana.

Advertisement

Brighton ce ta fara cin kwallo ta hannun Pascal Gross saura minti 15 a tafi hutun rabin lokaci, sannan shi ne ya kara ta biyu da tazarar minti tara tsakani.

Pascal Gross ya ci Manchester United kwallo shida a Firimiyar Ingila shi kadai – shi ne kan gaba dan wasan Brighton da ya ci United kwallaye da yawa a gasar.

Advertisement

United ta zare daya bayan da aka dawowa daga hutun rabin lokaci, bayan da Alexis Mac Allister ya ci gida, saura minti 22 a tashi daga wasan.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyoyin suka buga wasan bude Firimiyar wato makon farko a tsakaninsu.

Advertisement

A kakar da ta wuce, Brighton ta doke United 4-0 ranar 7 ga watan Mayu, bayan da tun farko United ta ci Brighton 2-0 a ranar 15 ga watan Fabrairun 2021.

Ita kuwa Manchester City mai rike da kambun Firimiyar Ingila, ta fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke West Ham United da ci 2-0 ranar Lahadi.

Advertisement

Sabon dan wasan da City ta dauko a bana, Erling Haaland, shi ne ya ci mata kwallon farko a bugun fenareti, kuma shi ne dai ya kara ta biyu a raga.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending