Connect with us

News

Yau kotun ƙoli za ta saurari ƙarar da jihohi su ka shigar kan soke wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi

Published

on

 

 

A yau Laraba ne ake sa ran kotun ƙolin Najeriya za ta saurari dukkanin ɓangarori a ƙarar da wasu gwamnonin johohi suka shigar domin hana Babban Bankin Najeriya aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin naira na 1,000, da 500, da kuma 200.

 

Gwamnatocin jihohin Kaduna, da Zamfa da kuma Kogi ne suka shigar da ƙarar, inda tun farko kotun ta bayar da umurnin jingine wa’adin daina amfani da takardun kuɗin na 10 ga watan Fabrairu, wanda bankin ya bayar a farko.

An umarci sanatoci biyu mata su fice daga majalisa kan ‘tufafin da suka saka’

BBC ta rawaito cewa mutane dai a Najeriya sun shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira 1,000, da 500, da 200 duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.

Advertisement

 

Haka nan rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin na Najeriya.

 

Haka nan ma wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.

 

Jama’ar ƙasar na sanya ido kan abin da kotun za ta ce a zamanta na yau, wanda zai iya yin tasiri kan halin da al’ummar ke ciki na ruɗani game da ci gaba ko kuma daina amfani da tsofaffin kuɗaɗen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending