Connect with us

News

Zargin cin zarafin Naira:Kotu ta bayar da belin Jarumar noollywood a kan miliyan 5

Published

on

 

 

Kotu ta bayar da belin wata ‘yar fim, Oluwadarasimi Omoseyin a kan kudi naira miliyan 5, a kan tuhumar ta da laifin cin zarafin naira.

 

An kama ta ne bayan wani faifan bidiyo dake yawo a shufukan sada zumunta nida take liki da sabbin takardun kudin Naira da aka yi wa gyaran fuska a wani biki

 

An kashe mutum hudu ciki har da mace mai shayarwa, a rikicin karancin sabbin kudi a jihohin

A cewar mai gabatar da kara na EFCC S. I. Sulaiman, laifin ya ci karo da sashe na 21 (1) na dokar CBN na shekarar 2007.

Advertisement

 

Alkalin kotun ya bayar da umarnin tsare wanda ake kara a gidan yari har sai an yanke shawarar neman belin ta.

 

A ci gaba da shari’ar a ranar Laraba, kotun ta amince da bukatar Omoseyin, wanda lauyanta, Adenike Goncalves ya shigar.

 

Mai shari’a Aneke ta amince da bayar da belin jarumar a kan kudi naira miliyan 5

Advertisement

 

 

Mai shari’a Aneke Ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 3 ga Afrilu domin yi masa shari’a.

 

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kama Omoseyin a ranar Laraba, 1 ga Fabrairu, 2023 a kan titin Awolowo, Ikoyi, Legas, kuma ta mika shi ga EFCC domin bincike.

Advertisement

 

An kama ta ne bayan wani faifan bidiyo na zarginta da fesa tare da taka sabbin takardun kudin Naira da aka yi wa gyaran fuska a wani biki da ya bayyana a yanar gizo.

 

 

 

 

Advertisement

The Nation

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending