Liverpool za ta karbi bakuncin Real Madrid ranar Talata a wasan farko zagayen ‘yan 16 a Champions League da za su kara a Anfield.
Wannan shine karo na 10 da za su kece raini a tsakaninsu, Real Madrid ta ci biyar da canjaras daya, Liverpool ta yi nasara uku.
Wasan karshe da suka fafata a tsakaninsu, shine a bara a Champions League, inda Real ta ci 1-0 a Faransa ta lashe Champions League na 14 jimilla.
Karo na 12 da Jurgen Kloop da Carlos Ancelotti za su fuskanci juna, inda kociyan Real ya yi nasara biyar na Liverpool ya ci uku da canjaras uku.
Ancelotti ya ja ragamar AC Milan da Real Madrid suka lashe Champions League bibiyu kowacce, Kloop ya dauki kofin zakarun Turai a Liverpool a 2018/19.
Real Madrid mai Champions League 14 tana ta biyu da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona a La Liga.
Liverpool mai kofin zakarun Turai shida tana ta tara a teburin Premier League da maki 35.
