News
Kotun Daukaka Kara ta amince da bukatar INEC, Ta yi watsi da Bukatar Obi.
Kotun daukaka kara da ke Abuja, a ranar Laraba, ta yi watsi da bukatar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Gregory Obi na neman hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC sake fasalin na’urorin BVAS da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Daily Post ta ruwaito cewa, Kotun ta ce amincewa da bukatar hakan zai kawo cikas ga hukumar zaben a gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris.
YANZU-YANZU: Manya lauyoyi masu muƙamin SAN su 19 sun lashi takobin taimakawa Atiku kyauta
Kotun ta amince da INEC cewa an shigar da bayanan amincewa da ke kunshe a cikin na’urorin BVAS a cikin Babban kundinta na adana bayanau kuma ana iya samun su a kowane lokaci.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da yarjejeniyar da ta yi da INEC a kan cewa ba a kalubalanci duk wasu kura-kurai da aka yi a cikin takardar shaidar hukumar zabe ba.
Kotun ta ci gaba da cewa, ikirarin da INEC ta yi na cewa ba za a iya yin katsalandan a kan bayanan ta dake cikin na’urorin BVAS ba a lokacin da ta ke saka bayanan, ba Obi nr ya kai hari ba, don haka ake ganin sahihai ne.
