News
INEC Ta Wallafa Sakamakon Zabe 66,600 A Shafin IRev
Kawo yanzu, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya sakamako sama da 66,634 na zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha da aka gudanar ranar Asabar a shafin tattaara sakamakon zabe na iReV.
Zuwa lokacin kammala wannan labari, INEC ta sanya sakamako 66,634 a shafin, daga jihohi 28 da aka yi zaben na ranar Asabar.
BADGE ta Taya bola tinubu murnar lashe zaben shugaban cin kasa.
Wannan wani ci gaba ne, sabanin zaben shugaban kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda aka samu jinkirin sanya sakamakon a iRev.
iRev shi ne shafi na musamman da INEC ta tanada domin wallafa sakamako tun daga rumfar zabe, ta hanyar amfani da na’urar tantance masu zabe ta BVAS, bayan jami’an zabe da wakilan jam’iyyu sun sanya hannu a kan takardar sakamakon.
Tsaikon da aka samu a wancan karon ya haifar da surutai a yayin da jam’iyyun adawa suka ki karbar uzurin hukumar game da tangardar da shafin ya samu.
Daily Trust ta ruwaito cewa Hasali ma, sun bukaci a soke zaben gaba daya, ko da yake INEC ta yi watsi da bukatar.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
