News
Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe ya rasa kujerarsa a hannun Lawan Musa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Honarabul Ahmed Mirwa Lawan, ya rasa kujerarsa a hannun Lawan Musa mai shekaru 35 dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Nguru II.
Jami’in zaben na jihar, Dakta Habib Muhammad, wanda ya bayyana sakamakon zaben ya ce Musa ya samu kuri’u 6,648 inda ya kayar da kakakin jam’iyyar APC na Yobe wanda ya samu kuri’u 6,466.
NNPP ta bukaci a soke zaben gwamnan Borno
Ya ce sauran ‘yan takarar ADC da NNPP da APM sun samu kuri’u 3,023 da 14 bi da bi.
Daily Trust ta ruwaito cewa Kakakin Majalisar Yobe ya kasance a majalisar tun 2003 lokacin da aka zabe shi a matsayin dan majalisa a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
Advertisements
