Connect with us

News

Sarkin Kano Ya sake nada wasu sababbi Hakimai guda hudu tareda daga Darajar wasu Hakimansa guda shida.

Published

on

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, Ya sake nada wasu sababbi Hakimai guda hudu tareda daga Darajar wasu Hakimansa guda shida.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa daya rabawa manema labarai a Kano

Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace an nadasu Sarautun ne bisa cancantar da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

 

Yadda Ganduje ya kore mu daga APC haka mu ka sallame shi a siyasar Kano

Wadanda aka nada din sunbhadar da Alhaji Nura Sunusi a Matsayin Dan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a Matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a Matsayin Kaigaman Kano.

Advertisement

Sai kuma Hakiman da aka ciyar dasu gaba sun hada da Malam Umar Sunusi Bunun Kano ya koma Dan Makwayyon Kano da Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano zuwa Dan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.

Saura Hakiman da aka ciyar dasu gaba sune Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zamnan Kano zuwa Dan Madanin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Magayakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Dankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP, ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tareda gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tareda Sanya tsoron.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending