Connect with us

News

Gobara ta tashi a kasuwar ‘Yan Katako dake Zaria

Published

on

 

 

 

Gobara ta tashi a kasuwar ‘Yan Katako ta Sabon Gari a birnin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da daddare zuwa wayewar garin Laraba

Wani mai shago a kasuwar Idris Mai Kusa ya shaida wa TRT Afrika cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe biyu na dare.

Advertisement

 

Gwamnatin Taraiyya Zata Yanke Alakar Dake Tsakaninta Da Wasu Kanfanonin Samar Da Lantarki

Babu tabbaci kan kan me ya jawo gobarar sai dai ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa ta.

 

“An kira ni da misalin karfe biyun dare aka ce mani an kawo wuta sai kawai wani turken wuta ya yi tartsatsi a kusa da wuraren da shagunanmu suke, daga nan ne wutar ta tashi,” kamar yadda Idris ya shaida wa TRT Afrika.

 

“Ko lokacin da na kira kasuwa domin na ji wane hali ake ciki, shagunanmu sun riga sun kone,” in ji Idris.

Advertisement

 

Ya bayyana cewa motar kashe gobara guda daya ta je kasuwar domin kashe wutar amma lamarin ya gagare ta saboda wasu matsaloli.

 

Ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani mutum da zai iya kididdige yawan asarar da aka tafka sakamakon wannan gobarar, amma ya ce akwai shaguna da dama da suka kone.

 

“Kayan da ke cikin shagonmu kadai wadanda suka kone a iya lissafi za su iya kai na miliyan18, wasu shagunan ma sun fi mu asara,” in ji Idris

Advertisement

 

Ya bayyana cewa bisa kiyasi shaguna sama da 100 sun kone sakamakon wannan gobarar.

 

Shi ma Sani Yusuf Dace wanda a kasuwar ta ‘Yan Katako yake ya shaida wa TRT Afrika cewa sun tafka asarar da ba ta misaltuwa.

 

“Allah ne ya jarabce mu, daga Allah ne kuma mun bar masa, Allah ya musanya mana da alkhairi,” in ji Sani.

Advertisement

 

Ya bayyana cewa lissafin iya dukiyar da aka yi asara sai an zauna saboda a cewarsa asarar tana da yawa.

 

Shi ma Rabi’u na Alhaji Ahmadu da ke kasuwar ya shaida cewa sun yi asara ta miliyoyi sakamakon wannan goabara.

 

Ya bayyana cewa wannan kaddara ce da Allah ya aiko musu kuma sun dauki kaddarar.

Advertisement

 

Hukumomi dai ba su ce komai ba tukuna dangane da wannan gobara.

 

Ana yawan samun gobara a kasuwanni a Nijeriya inda ko a baya-bayan nan sai da aka yi gobara a Kasuwar Kurmi ta Kano da kuma babbar Kasuwar ‘Monday Market’ ta Maiduguri.

 

Haka ma an yi mummunar gobara a kasuwar Balogun da ke Legas

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending