News
Yan sanda sun kama matasa uku da kilo din wiwi 812.5 a Nijar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jami’an hukumar ‘yan sanda mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi wato OCRTIS a Jamhuriyyar Nijar, ta yi nasarar kama wasu matasa uku a garin Gaya na Jihar Dosso dauke da daurin tabar wiwi 917 da nauyinta ya kai kilogiram 812.5.
Wannan kame na zuwa ne kasa da mako guda bayan hukumomi sun yi makamancin wannan kamen a kasar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta ce an kiyasta kudin wiwi din inda ya kai CFA 36,680,000, kwatankwacin dala 62,000.
An shigar da wiwi din ne ta hanyar Kogin Isa cikin garin na Gaya na kan iyakar Jamhuriyyar Benin da Nijeriya, inda matasan suka yi niyyar jigilarta zuwa Nijeriya da wasu garuruwa na kasar Nijar.
Jaridar trt africa ta ruwaito cewa Masu sharhi na cewa masu safarar miyagun kwayoyi na son mayar da Jamhuriyyar Nijar hanyar tsallakawa da hajojinsu zawu wasu kasashen yamma.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta kasar, Abou Mountari ya ja hankalin ‘yan kasar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron hadin kai don yakar masu wannan “muguwar sana’ar”.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
