News
Shugaban kasa muhammad buhari zai ƙaddamar da Titin Kano zuwa Abuja a yau talata
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta samar a sassa daban-daban na Nigeria.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai ɗauke da sa hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina.
Lokaci Ya Kure Buhari Ba Zai Iya Karawa Ma’ikata Shekarun Ritaya Ba – Ministan Kwadago
Sanarwar ta ce, cikin ayyukan da shugaba Buhari zai ƙaddamar har da wani sashe na titin Kano zuwa Abuja da aka kammala aikinsa.
Sauran sune: Gadar Naija ta biyu da ta haɗa biranen Asaba dake jihar Delta da Onitsha dake jihar Anambra, gadar Loko-Oweto dake tsakanin jihohin Nassarawa da Benue, sakatariyar gwamnatin tarayya dake Awka a jihar Anambra, sakatariyar gwamnatin tarayya dake Gusau a jihar Zamfara.
Sauran sune: sakatariyar gwamnatin tarayya dake Yenagoa a jihar Bayelsa, da kuma gadar Ikom dake jihar Cross River.
