Sports
Ronaldo ya zama dan wasan kwallon kafa na farko da ya buga wasanni 200 a duniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo, ya zama dan wasan kwallon kafa na farko na maza da ya buga wasanni 200 na kasa da kasa, bayan da ya taka leda a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Iceland a ranar Talata.
Ronaldo ya fara taka leda a duniya a shekara ta 2003.
Hukumar EFCC Ta Saki Ortom Bayan Sa’o’i 10
Dan wasan mai shekaru 38 kuma shi ne kan gaba wajen zura kwallo a raga a gasar kwallon kafa ta duniya da kwallaye 122.
Dan wasan gaba na Al Nassr kuma shi ne mutum daya tilo a tarihi da ya taka leda a gasar cin kofin nahiyar Turai guda biyar.
A gasar cin kofin duniya ta 2022 da aka yi a Qatar, Ronaldo ya zama dan wasan kwallon kafa na farko da ya ci kwallo a gasar cin kofin duniya daban-daban guda biyar.
Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, Ronaldo yana da manyan karramawa guda biyu tare da Portugal – ya jagoranci kasarsa zuwa ga nasara a gasar Euro 2016 da gasar cin kofin UEFA Nations League shekaru uku bayan haka.
Yayin da Ronaldo ke rike da kambun tarihi idan aka zo batun wasannin kasa da kasa na maza, wanda tsohon USWNT ne ya rike shi da kuma 2015 U.S. Soccer Hall of Fame inductee Kristine Lilly da wasanni 354.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
