Connect with us

News

Shehu Sani Ya Maida Da Martani Kan Karin Albashin Tinubu, Shettima Da Sauran Su

Published

on

DAGA  YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta fara karawa ma’aikata karancin albashi mafi karanci a kasar.

Sani ya bayyana hakan ne biyo bayan shirin kara albashin zababbun ‘yan siyasa da suka hada da shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da kuma masu rike da mukaman shari’a da na gwamnati.

Advertisement

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Sani ya rubuta cewa, “Ya kamata a kara mafi karancin albashin ma’aikata a gaban na manyan masu rike da mukaman gwamnati.

bai kamata ace duka masu rike da manyan mukaman Najariya 3 duk su fito daga kudu ba.—Yari

“Da wannan karin kashi 114%, dan majalisar tarayya zai rika karbar albashin kusan Naira miliyan 2 duk wata da kuma Naira miliyan 25 a duk wata ga ofishinsa. Kudaden da aka samu daga cire tallafin ya kamata a kashe su cikin hikima.”

Advertisement

A baya dai DAILY POST ta rahoto cewa hukumar tattara kudaden shiga da raba kudi da kuma kasafin kudi ta yi kira da a kara albashin zababbun ‘yan siyasa da suka hada da shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da ma’aikatun shari’a da na gwamnati da kashi 114 cikin 100 masu rikewa.

RMAFC tana da alhakin tantance albashin da ya dace ga masu rike da mukaman siyasa, wadanda suka hada da shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, mataimakan gwamnoni, ministoci, kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, ‘yan majalisa da masu rike da ofisoshin da aka ambata a sashe na 84 da 124 na wannan Kundin Tsarin Mulki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending