Connect with us

News

Jerin Sunayen Masu Mukamai 10 A Lokacin Buhari Da Ya Kamata Tinubu Yasa ayi Bincika akan su

Published

on

Shugaban kasa bola Ahmad tunibu da Timi Frank

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa Timi Frank, ya buƙaci shugaba Tinubu ya binciki wasu masu manyan mukamai a tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Timi Frank ya ce ya kamata Tinubu ya gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin ofishin wasu daga cikin su, kuma kada a bari su guje wa hukunci.

Hukumar tsaro ta DSS ta bankaɗo barazanar kai hare-hare lokacin bukukuwan sallah

Fimi Frank ya bayyana sunayen ‘yan majalisar ministocin Buhari da ya kamata su kasance a komar Hukumomin EFCC da Kuma  DSS.

Advertisement

Ya ce ya kamata a binciki Timipre Sylva, da Sanata Hadi Sirika da Abubakar Malami da Mele Kyari da Sadiya Umar Farouq da Hadiza Bala Usman Kanar Hammid Ali.

Sauran sun hada da – Babban jami’in Hukumar Kula da Tsaron Ruwa ta Nijeriya Bashir Jamo, da Tsofaffin manajojin daraktoci da shugabannin Hukumar Raya Yankin Neja-Delta NDDC da duk shugabannin tsaron da aka yi wa ritaya cikin kwanakin nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending