Connect with us

News

NiMET ta yi Hasashen Samun Hadari Da Tsawa A arewacin Najiriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet, ta yi hasashen samun yanayi na hadari da kuma tsawa tsakanin Juma’a da Lahadi a fadin kasar.
Hakan ya zo ne bisa hasashen yanayi na hukumar NiMet da aka fitar ranar Alhamis a Abuja wanda ya yi hasashen za a yi hadari a yankin arewa tare da yiwuwar samun tsawa.

Jerin Sunayen Masu Mukamai 10 A Lokacin Buhari Da Ya Kamata Tinubu Yasa ayi Bincika akan su

Haka Kuma Wasu daga cikin Jihohin da ake sa ran sauyin yanayin zai shafa sun hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Kaduna, Taraba da Adamawa”.
NiMet ta lura cewa ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Borno, Adamawa, Kano, Bauchi, Kebbi, Zamfara, Katsina, Gombe, Jigawa da Taraba.
Hukumar ta yi hasashen tsawa a fadin yankin a lokutan rana da yamma.

Advertisement

Ana sa ran samun washewar sararin samaniya a yankin Arewa ta tsakiya inda ake sa ran za a yi ruwan sama a sassan Kwara, Neja, Kogi da kuma Babban Birnin Tarayya.

Hukumar NiMet ta yi hasashen sararin samaniya a ranar Lahadi mai karancin gizagizai a yankin arewa tare da yiwuwar samun ‘yan tsawa a sassan jihohin Bauchi, Adamawa, Taraba, Jigawa, Borno da Gombe da safe.

Advertisement

Akwai yiwuwar tsawa a sassan Niger, Kwara, Benue, Kogi, Plateau da kuma babban birnin tarayya Abuja da rana ko yamma.

A cewar NiMet, a yankunan da ake sa ran za a samu tsawar, ana iya samun iska mai karfi kafin ruwan sama, don haka.

Advertisement

A don haka ake shawartar jama’a da su yi taka tsantsan.

Sannan ta shawarci jama’a da su kasance a cikin gida musamman a lokacin da ake ruwan sama mai yawa domin gujewa abin da kaje ya zo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending