News
Matsan garin Geidam Masu amfani Facebook zasu gudanar da gagarin taron sada zumunta karo na farko.
DAGAaISHAQ ISMA’IL ALIYU
Taron hada kan Matasa masu amfani da kafar sadarwar na zamani Facebook, wanda zai samar da hadin kan Matasa da sanin juna,da kokarin ganin gyaran makomar Matasan karamar hukumar Geidam da yin zumunchi, tare da shawarwari daga masana kan yadda Matasa da masu amfani da kafar Sadarwa ta Yanar Gizo Gizo zasu mori amfani da ita wajen kawo cigaba da hadin kai, da kuma wayar da kan jama’a
Yana da matukar muhimmanci sosai ga jama’a musamman matasa masu amfani da kuma ma’abota wannan kafa mai albarka, halartar wajen wannan gangamin taro da aka shirya don inganta kyakkyawan alaka tsakanin Matasan wannan karamar hukuma tamu mai Albarka ba tare da nuna wariya banbancin ra’ayin Jam’iyyu ba, zai kawo kyakkyawan alaka da fahimtar da juna.
Jami’ar Bayero ta yi karin kudin makaranta da dakunan kwanan dalibai
Sannan Mafi yawancin al’ummar dake amfani da wannan kafa bakowa yasan kowa ba, Don haka za’a hadu don kara Dankon zumunchi da inganta Alaka mai karfi tsakanin Matasa da suke amfani da wannan kafa ta Facebook, sannan za’a fitar da manyan abubuwa masu muhimmanci da manyan mutane daga mabanbanta wurare na wannan yanki za’a gabatar da mahimman abubuwa dan inganta rayuwar Matasan wannan karamar hukuma
Taron dai zai gudana a Ranar juma’a 30/June/2023 wajen taro Even center Geidam
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
