Connect with us

News

Umarnin CBN Kan Soshiyal Midiya Ya Saɓa Doka – NDPC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

Hukumar kare bayanan sirrin masu amfani da intanet ta ƙasa (NDPC), ta ce umarnin da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya bai wa bankuna na neman bayanan soshiyal midiya na abokan hulɗarsu ya saɓa doka.

A ranar 26 ga Yuni ne CBN ya umarci bankuna da su riƙa karɓar bayanan soshiyal midiya na abokan hulɗarsu domin ƙara samun cikakkun bayanai game da su.

CBN ya ce hakan zai taimaka wurin yaƙi da halatta kuɗaɗen haram da kuma hada-hadar ta’addanci.

Advertisement

Sai dai a wata sanarwa da hukumar NDPC ta fitar ranar Alhamis ɗin nan ta ce ta na tattaunawa da CBN game da sanarwar.

Kwamishinan ƙasa na Hukumar Vincent Olatunji ne ya sa hannu a sanarwar.

A cewarsa babu wani dalili da za a nemi bayanan soshiyal midiya na masu hulɗa da bankuna amma idan CBN ya gamsar da su, to za su nuna masa matakan da ya kamata ya ɗauka kafin fara neman bayanan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending