Connect with us

News

Mutane uku ne suka rasa rayukansu  a wani hatsarin da ya faru a hanyar Legas zuwa Ibadan.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da daya ya samu rauni a wani hatsarin da ya faru a hanyar Legas zuwa Ibadan, a yau  Juma’a.

Advertisement

Hadarin dai ya hada da wata mota kirar Toyota Sienna mai lamba BDG 426 HT da wata mota kirar DAF mai lamba RNG 558 XC.

Za Mu Ɗau Mataki Kan Hudu Ari bayan kammala Bincike – INEC

Daily trust ta rawaito cewa direban Sienna ya kutsa cikin motar DAF da ke fitowa daga wurin tirela.

Advertisement

Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta.
Okpe ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a kusa da gidan mai na Total dake kan babbar hanyar.
A cewarta, mutane bakwai ne suka hada da manya maza hudu, manya mata biyu da yaro daya.
Okpe ya alakanta musabbabin hadarin da gudu daga bangaren direban Sienna.
“An kai wanda aka jikkata zuwa babban asibitin Isaara domin kula da lafiyarsa yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na FOS, Ipara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending