Connect with us

News

Za Mu Ɗau Mataki Kan Hudu Ari bayan kammala Bincike – INEC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce za ta ɗau mataki kan dakataccen kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Hudu Ari.
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Festus Okoye ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels.

 

Shugabanni: Ku Guje Wa Rayuwar Almubazzaranci Domin Nijeriya Ta Ci Gaba

Hudu Ari dai ya jawo hatsaniya lokacin da ya bayyana Sanata Aishatu Ɗahiru Binani a matsayin wacce ta yi nasara a zaɓen da ba a kammala ba.
Hakan ta sa shugaban ƙasa na lokacin, Muhammadu Buhari ya bada umarnin a binciki duk kan jami’an tsaron da ke da hannu cikin lamarin.

Mr Okoye ya ce “Ƴan sanda sun gama bincikensu kuma nan da makonni kaɗan za a sanar da ƴan Najeriya abinda aka gano.

Advertisement

“A bisa doka, INEC ce za ta shigar da ƙararsa don haka za mu ɗau mataki da zarar ƴan sanda sun miƙa mana sakamakon binciken.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending