Connect with us

News

Wani mutum ya mutu yayin satar Kayan Lantarki’ a cikin Taransufoma A Zariya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wani mutum da ake zargin mai sace kayan na’urar rarraba hasken lantarki (taransufoma) ne ya mutu lokacin da ya shiga cikin na’urar a unguwar Wusasa da ke Zariyan Jihar Kaduna.
Bayanai sun ce na’urar dai ita ce take ba Unguwar Kuregu da ke Wusasan wutar lantarki, kuma ya mutu ne yana kokarin yin sata a ciki.
Matashin dai ya gamu da ajalinsa ne da misalin karfe 4:00 na safiyar Lahadin da ta gabata, in ji mazauna yankin.

Yan daba sun kashe wani jami’in dan sanda a kano.

A cewarsu, sun sanar da Mai Unguwa abin da suka gani kafin daga bisani aka sanar da ofishin yanki na Rundunar ’Yan Sanda da ke Dan Magaji, a Zariya.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa Jami’an ’yan sandan dai daga bisani sun dauki gawar matashin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya domin ajiya.

Sarkin Wusasa, Injiniya Isiyaku ya tabbatar wa da wakilinmu cewa ko a makon da ya gabatasai da barayin suka sace kayan daya daga cikin na’urorin unnguwar.

Advertisement

Ya ce wannan karon Allah ne ya kama musu shi, sai dai suna zaton abokan satar nasa sun tsere. Ya ce har yanzu ba su iya gane daga inda mutumin ya fito ba ko wanda ya san shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending