Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air daga zirga-zirga nan take.

Published

on

 

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa NCAA  ta dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air daga zirga-zirga nan take.

Advertisement

Cikin wata wasika da daraktan hukumar, Kyaftin Ibrahim Bello Dambazau ya aikewa kamfanin, ya ce an dakatar da ayyukan kamfanin saboda matsalolin da ake samu da jiragen kamfanin samfurin Boeing BB737.

Kotu ta umurci hukumar DSS da ta gurfanar da Emefiele ko kuma ta saki shi cikin kwanaki bakwai

Daraktan ya ce hukumar ta kafa kwamitin bincike da za su tantance ingancin jiragen saboda ba za a kyale kamfanin ya ci gaba da amfani da jiragen Boeing 737 ba har sai bayan kammala binciken.

Advertisement

Ya ce daga matsalolin akwai lalacewar tayar jirgin na Max Air da ya tashi daga Yola zuwa Abuja da kuma gurbatar mai da aka samu a wani jirgin irinsa da ya haddasa wutar lantarkin jirgin ta ki aiki a filin jirgin saman Yola a ranar 7 ga Mayun 2023.

Haka kuma injin wani jirgin nasu na 737 ya sami matsalar daukar zafi a ranar 11 ga Yulin 2023 a tashar jiragen saman Malam Aminu Kano, abinda ya sa jirgin ya kasa tashi.

Advertisement

Sai kuma saukar gaggawa da wani 737 din ya yi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja saboda daukar zafi a mazaunin matukin jirgin a ranar 11 ga Yulin 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending