News
Hukumar WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 262,803
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar shirya jarrabawar ƙasashen yammacin Afrika (WAEC) ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 262,803 da suka rubuta jarrabawar kammala sakandare ta 2023.
Shugaban ofishin hukumar a Legas, Patrick Areghan, ya ce an rike sakamakon jarrabawar ne bayan samun dalibai da tafka maguɗi a matakai daban-daban na jarabawar.
Kasar nan Ce Kan Gaba A Bangaren Masu Zaman Kashe Wando A Duniya
Ya ce kashi 16.29 na jimillar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar ne lamarin ya shafa.
Mista Areghan ya yi bayanin cewa “dailan samun irin wannan matsala a bayyane suke, ɗalibai ba su zage damtse suka yi karatu ba, inda suka dogara da satar amsa a yayin jarrabawa.”
Bbc Hausa ta rawaito cewa ɗaliban da lamarin ya shafa suna da zaɓin gabatar da kansu don bincike da kuma neman damar wanke kansu daga wannan zargi na tafka maguɗin jarabawar, kamar yadda aka saba yi a baya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
