Connect with us

News

Zanga-Zanga Ta Barke A Kano Kan Yunkurin Daukar Matakin Soji A Jamhuriyyar Nijar.

Published

on

Breaking news indaranka

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Wasu masu zanga-zanga sun mamaye tituna a Jihar Kano suna bayyana adawa da yunkurin daukar matakin soji kan wadanda suka yi juyin mulki a Jamhuriyyar Nijar.

A kwanan nan ne Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta bai wa dakarunta umarnin zama cikin shirin ko-ta-kwana domin warware tankiyar da ta kunnu a kasar da ke makwabtaka da Najeriya.

Advertisement

Ranar Matasa Ta Duniya: kalubalen da matasa ke fuskanta a kasar nan.

Rahotanni na nuni da cewa, masu zanga-zangar dauke da tutocin Najeriya da Nijar sun fito a wannan Asabar suna masu bayyana adawarsu kan shirin tura dakarun Jamhuriyyar Nijar.

A yayin da suke tattaki a Kano, suna yekuwar cewa “al’ummar Nijar ’yan uwanmu ne da an riga an zama daya.

Advertisement

“Da mu da mutanen Nijar babu bambanci, ba ma son yaki.

“Daukar matakin yaki a Nijar rashin adalci ne da Turawan Yamma suka kitsa.”

Advertisement

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kiraye-kiraye da gargadin daukar matakin soji a Nijar, musamman daga Arewacin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending