News
Ranar Matasa Ta Duniya: kalubalen da matasa ke fuskanta a kasar nan.
DAGA ABDULKADIR MUHAMMAD TUKUNTAWA.
A ko wacce Rana irin ta yau ake gudanar da bikin ranar matasa ta duniya Wanda majalisar dinkin duniya ta ware ta domin irin muhimmancin da matasa suke dashi a cikin al’umma.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa yawancin matasa a halin yanzu basa shiga ana damawa dasu ne a harkar siyasa da kuma lamuran yau da kullum sunfi mai da hankali ga harkar kasuwanci da kuma wasu ayyuka mabanbanta.
Gwamnatin Kano Ta Fara Tattara Kauyuka Da Garuruwa Masu Matsalar Lantarki – Injiniya Sani Bala
Jaridar indaranka tattaro cewa Matasa suna kokawa ta hanyar karatunsu tare da fatan neman aiki mai inganci da ma’ana wanda za su yi amfani da shi don biyan bukatun kansu da danginsu amma ba haka lamarin yake ba.
Tsoffinmu sun ki yin ritaya. Sun ci gaba da karyata shekarun su domin rike aikinsu alhali ‘ya’yansu, musamman masu karatun digiri suna yawo ba tare da aiki ba.
Tunda an ce ‘zaman kashe wando yana sa miyagun tunani’ shi ya sa wasu lokutan matasa kan shiga ayyukan masha’a kamar sace-sace, yahoo-yahoo, tsafi da sauransu.
Matsalar shaye-shaye tana ci gaba, kuma har yanzu babbar matsala ce da ke addabar matasan Najeriya.
Alkaluma sun nuna cewa wasu matasa sun rungumi shaye-shaye ne domin huce takaicin matsalolin rayuwa lamarin da kan tagayyara su.
Matsalar kwayoyi da shan wiwi har yau cuta ce da ke aukuwa tsakanin matasa a yayin da ake hana mutum guda, biyu zasu taso. Hakan ya shafi mata da maza.
“A cikin matsololin da matasa ke fuskanta, shaye-shaye duk ya fi muni. Matasa, mata da maza sun koma ga dogaro ga kwayoyi da sauran abubuwa masu cutarwa wadanda sun zama abin samu cikin sauki a duniya,” Faraz Muhammad ya ce.
“Ba wani sabon abu ba ne domin ya dade yana faruwa, kuma wadatar fahasa da kuma sha’awar matasa, sun sa ana sauƙin samun yanzu fiye da shekaru goma da suka gabata,” a cewarsa.
