Connect with us

News

Bai Kamata Ba Tunibu Ya Baiwa Dan Siyasa Ministan Tsaro Ba-Shehu Sani

Published

on

Shehu sani

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Tsohon dan majalisar dattawa dake jahar Kaduna Sanata Shehu Sani ya soki shugaba Bola Ahmad Tunibu kan nada Mohammed Badaru a matsayin ministan tsaro.

Tsohon sanatan jahar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce bai kamata Tinubu ya nada dan siyasa a matsayin ministan tsaro ba ana cikin wannan yanayi na karancin tsaro a kasar nan.

Advertisement

Gwamnatin jahar Kano Ta Kaddamar Da Kwamitin Tantance Ma’aikata Kusan Dubu 10 da 800

Sani ya ce kamata ya yi a baiwa wani jami’in soja mai ritaya wanda yayi aikin soja kuma yasan minene tsaron kasa wanda kuma keda bayanan nasarorin da aka samu da wadanda ba’a samu ba.

Kamar yanda Sani ya rubuta a shafin Twitter cewa duba da kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta, na ga ya kamata Ministan tsaro ya zama jami’in soja mai ritaya mai gogewa da kuma tarihin nasarori.

Advertisement

Wannan ofishin bai kamata ya zama siyasa kawai ba, musamman a wannan lokacin da mafi yawan mutanen kauyuka basu iya kwana da ido biyu a rufe.

Inda suke fargabar afkowar barayin daji da ke sace mutane don karbar kudin fansa ko kuma su kwashi duk wani abinda ka mallaka Ba tare da wani ya hana su

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending