Sports
Real Madrid ba za ta sayi Mbappe ba – Ancelotti
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce ba zai sayi ɗan wasan gaba Kylian Mbappe daga Paris St-Germain a bana ba.
Mbappe, ɗan shekara 24 ya zuwa yanzu ya ƙi rattaba hannu a kan kwantiragi da PSG, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗin cewa zai koma ƙungiyar ta La Liga.
Najeriya Ce Kasa Ta 11 A Yawan Masu Amfani Da Yanar Gizo A Duniya
Ana tunanin cewa PSG a shirye take ta sayar da kyaftin ɗin na Faransa, maimakon yin kasadar rasa shi kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a shekara mai zuwa.
Da aka tambaye shi game da yarjejeniyar Mbappe, Ancelotti ya ce “A’a, na yanke hukunci 100%.”
Mbappe ya shafe tsawon lokaci yana atisaye, ba tare da ‘yan wasan PSG ba a wannan wata sakamakon taƙaddamar kwantiraginsa, amma ya dawo bayan tattaunawa da mahukuntan ƙungiyar.
An ajiye shi a wasan farko da kulob ɗin ya buga da Lorient, amma ya zura ƙwallo a raga bayan ya shigo daga baya a wasan da PSG ta tashi 1-1 da Toulouse a makon jiya.
