Connect with us

News

Yawan Hadiman Da Gwamnan Jahar Kano Ya Nada Yanzu Sun Kai 138

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada sabbin Hadimai 57 domin cike gurbin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka na musamman a gwamnatinsa.

Jaridar Indaranka ta rawaito cewa Ya zuwa yanzu, gwamnan ya nada adadin mataimaka guda 138 ke nan.

Advertisement

Majalisa za ta binciki ayyuka 10,000 da aka yi watsi da su

Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da daren jumma,a, inda ya ce sabbin nade-naden Hadiman 57 na daga cikin “kokarin Gwamnan na jan matasa a jiki”.

Wadanda da aka bai wa sabbin makaman sun hada da: bangaren Fasahar Sadarwa, Wayar da Kai, Watsa Labarai, Kula da Ayyuka, Ci gaban Kasuwanci da Tashoshin Mota.

Advertisement

 

 

Advertisement

Sauran bangarorin sun hada da; Kasuwanni, Fitilar Titin, Mawaka (Mawallafa), Al’amuran Kannywood, Kasuwar Waya, Makarantun Islamiyya, Tsaro, Harkokin Soja, Al’amuran Kasuwar Man Fetur, Karkara, Rediyo, Harkokin Ƙasashen waje, Ilimin Yara Mata, Ayyuka na Musamman I, Ayyuka na Musamman II da sauransu.

 

Advertisement

Bature ya ce, “Nade-naden za su fara aiki ne nan take, inda ya ce ana sa ran duk wadanda aka nada za su sauke nauyin da aka dora musu.

 

Advertisement

 

a ranar 16 ga watan Yuni ne gwamnan ya sanar da nadin mataimaka 14, yayin da kuma a ranar 18 ga watan Yuli gwamnan ya sake nada mutum 15 a matsayin masu ba da shawara na musamman ranar 7 ga watan Agusta ne gwamnan ya sanar da nadin mataimaka 42

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending