Connect with us

News

Rundunar Yan Sanda  Jahar Kano Sun Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Tunzura Jama’a Dake Farwa Wadanda Ake Ikirarin Masu Shan Jini Ne 

Published

on

Spread the love

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Rundunar Yan Sanda  Jahar Kano Sun Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Tunzura Jama’a Dake Farwa Wadanda Ake Ikirarin Masu Shan Jini Ne

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama Mutane 8 a unguwanni Kwana Hudu da Zango da kuma Hotoro bisa zargin tunzura jama’awajen farwa mutane da ba su ji ba ba su gani ba da ikirarin cewa masu shan Jini ne.

Gwamnatin Jahar  Kano Zata Kaddamar Da Rabon Tallafin Rage Radadi Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano ta gargadi al’ummar jihar kan wani zargin karya ko jita-jita da ka iya kaiwa ga hallaka rayukan Mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Rundunar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Abdullahi Harina Kiyawa ya fitar, ta ce ta samu labari daban-daban har guda uku a wurare mabambanta a jihar Kano inda ake zargin wadanda ba su ji ba ba su gani ba da kasancewa ‘yan kungiyar masu tsafi ko shan Jini.

Advertisement

A cewar sanarwar, wadanda al’amarin ya rutsa da su, sun sha bakar wahala har an kusan kashe su kafin ‘yan sanda su kai musu dauki a Kwana Hudu da Zango da Hotoro tsakanin ranakun 1 zuwa 3 ga watan Satumba.
Kiyawa yace yanzu haka ana kan gudanar da bincike, inda ya gargadi masu yada wannan jita-jita da su daina daga yanzu domin rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kamawa da gurfanar da mutanen da aka samu da hannu.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *