Connect with us

News

Gwamnatin Jahar  Kano Zata Kaddamar Da Rabon Tallafin Rage Radadi Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Published

on

Advertisements
ads

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

A yau ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da rabon kayan abinci a matsayin wani bangare na rage radadi, watanni uku bayan cire tallafin man Fetur da shugaban kasa a Bola Ahmad Tinubu ya yi.

Al’ummar Kano dai sun dade suna dakon matakan da za’a dauka na samar da saukin tsadar rayuwa, kuma a kwanakin baya wasu mata ma sun gudanar da zanga-zangar lumana suna neman a saukaka farashin abinci bayan da gwamnatin tarayya ta amince da Naira billiyan 5 ga kowace jiha.

Samar Da Asusun Sarrafa Shara A Kasar nan Zai Bunkasar Tattalin Arziki Da Inganta Muhalli – AWAMN

Sai dai a iya cewa jira ya kare a yanzu inda mai magana da yawun gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature ya tabbatar da safiyar yau a cikin wani gajeren sako da ya aike wa manema labarai cewa za a fara raba kayan abinci a yau.

Ya ce taron zai gudana ne a hukumar bunkasa aikin gonad a raya karkara ta Kano KNARDA da karfe 11 na safe ba tare da wani karin bayani ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending