Connect with us

Opinion

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO ENG. ABBA KABIR YUSUF

Published

on

 

Bayan gaisuwa irinta girmamawa da godiya bisa irin jajircewar ka a fannin da ya shafi cigaban jihar kano tun kafin nasarar jamiyyar NNPP a Jihar Kano.

Advertisement

 

Tabbas haki ka duba da kananun shekaru da kake dashi da kuma kudirorin shugaban ci hadi da manufa Masu kyau da kake dasu yasa Allah ya kawo ka wannan kujera ta kwamishinan Raya karkara na jihar kano.

Advertisement

Babu sauran adawa tsakanina da Messi – Cristiano Ronaldo

Bazan Kai da nisa ba duk Dan jihar kano yasan karamar hukumar Takai a fannin siyasa kuma yasan rawar ganin da karamar hukumar ke takawa wajen kafa geamnatoti tun kafuwar demukradiyya.

 

Advertisement

Mai girma Kwamishina sanin kanka ka San gudun mawar da alummar karamar hukumar Takai suka baiwa Jamiyyar NNPP da jagoranta Eng. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso wajen zazzaga masa kuriu masu tarin yawa a zaɓen da ya gabata na shugaban kasa, Hadi Dana gwamnatin da kakewa hidima a yanzu, wato gwamnatin jihar karkashin jagorancin Eng. Abba Kabir Yusuf.

 

Advertisement

Moriyar danukradiyya tana samun asali ne ta hanyoyi da dama Amma Babu kamar ace shugaba ya fita daga yankin ka, ko kuma karamar hukumar ka dama mazabar ka Baki daya.

 

Advertisement

Duk da banbanci siyasa alumma daga mazabu sun tayaka murnar zaman ka kwamishinan Raya karkara na jihar kano a mazabu goma Dake karamar hukumar Takai.

 

Advertisement

To kada ka Manta Mai girma Alhaji Hamza Safiyanu da akwai matsalolin Dake gaban ka wadda ya kamata tun bayan da aka rantsar dakai ka kafa kwamitin da zaiyi aiki a kananun hukumomin jihar kano Baki daya domin zakulo wadannan matsalolin a mikawa Mai girma gwamnan jihar kano Eng. Abba Kabir Yusuf domin taimakon alummar jihar kano, zuwa yanzu shiru kakeji.

 

Advertisement

To mu alummar Mazabar Durbunde Muna Mika wannan korafin namu da kukan mu ga Mai girma gwamnan jihar kano Eng. Abba Kabir Yusuf ta offishin Mai girma Kwamishinan Raya karkara na jihar kano Alhaji Hamza Safiyanu Kachako akan matsalar zaizayar kasa Dake Neman tashin alummar Mazabar Durbunde.

 

Advertisement

Mai girma gwamnan jihar kano ya kamata a duba wannan Lamarin domin matsala ce wadda ke bukatar taimako na gaggawa wadda idan ba ayi abinda ya dace ba to alumma na dab da rasa rayuka da dukiyoyinsu Hadi da abinci da suke nomawa.

 

Advertisement

Hakika munsan irin sadaukar duk da kalubale Dake gaban gwamnatin jihar kano Amma Hakan bai kamata ace an zubawa alumma ido akan barazanar rasa rayuka da muhalli ba.

 

Advertisement

Tabbas munada yakinin idan wannan wasika ta isa wajen da ya dace alummar Mazabar Durbunde zasu amfana da Dauki daga Mai girma gwamnan jihar kano Eng. Abba Kabir Yusuf.

 

Advertisement

Daga karshen Ina Mai adduar ubangiji Allah ya taimaki jihar kano, da karamar hukumar Takai gami da mazabar Durbunde ya kawo mana Zaman lafiya Baki daya.

 

Advertisement

Muhammad Usamat Suleiman Durbunde

Activist Journalist

Advertisement

Rock FM Radio Jalingo.

Taraba Truth and Facts Newspaper.

Advertisement

Northeast Times Newspaper.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending