Connect with us

News

Wasu ma’aikatan Babban Bankin Kasa CBN na amsar Albashi fiye da ministoci – RMAFC

Published

on

Hukumar tsara Albashi na kasa RMAFC
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar tsara Albashi na kasa RMAFC ta bayyana cewa a kwai wasu ma’aikatan Babban Bankin Najeriya da albashin su ya ɗara na Ministoci.

Shugaban Hukumar, Muhammad Shehu ya ce ba kamar yadda mutane ke zato ba, yan siyasa da dama ba su samun albashin kamar yadda wasu ma’aikatun gwamnati ke samu a Najeriya.

Advertisement

Ana Sa Ran Titin Layin Dogo Daga Kano Zuwa Maradi Nanda Shekarar 2025

Da yake hira da Kamfanin Dillancin Najeriya a Abuja, Shehu ya ce akwai ma’aikatan gwamnati dake amsar albashi fiye da ministoci da ‘yan majalisa a kasar nan, kuma ma’aikata ne kawai.

Ya ce rabon da aka rawa ‘yan siyasa Albashi tun 2007.

” Ina so in sanar wa ‘yan Najeriya ko albashin shugaban kasa bai kai naira miliyan 1.5 sannan na ministoci bai kan naira miliyan 1 ba.

Advertisement

” Na san wani ma’aikacin babban bankin Najeriya CBN, da ba ma darekta bane amma ya na karbar albashi fiye da minista.

” Akwai ma’aikata a NNPC, NCC da hukumar tashoshin ruwa na Kasar nan NPA da NIMASA da ke amsar albashi fiye da ministoci da yan majalisa har da gwamna ma.

Na san akwai wadanda ke korafin ‘yan majalisa na amsar kudade masu yawa, abinda basu sani ba shine wannan ba alabashi bane, wannan kedin hidima ce ta yau da kullum. Saboda akwai yan siyasa da ke karkashin su, a gundumomin su da sauran hidimomi.

Advertisement

Wani labarin kuma Ana Sa Ran Titin Layin Dogo Daga Kano Zuwa Maradi Nanda Shekarar 2025

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

Advertisement

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *