Connect with us

News

Kotu za ta raba gardama yau tsakanin Gawuna da Abba

Published

on

DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN 

A yau Laraba Kotun Sauraren Kararrakin Zabe za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano na 2023.

Advertisement

Jam’iyyar APC wadda tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ce ta kai karar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP kan rashin gamsuwa da sakamakon zaben gwamnan jihar.

Kwanaki 100: Kotun Zabe Ta Tsige ‘Yan Majalisar Wakilai 25, Sanatoci 5 Na APC, PDP, LP da NNPP

A yayin zaben da aka gudanar a watan Maris din 2023, Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’u 890,705.

Advertisement

Ana cikin zaman dardar a Kano tun bayan da aka sanar da ranar da za a yanke hukuncin.

Tun kafin a sanar da ranar, magoya baya daga duka bangarorin sun rinka zanga-zanga inda suke neman kotun ta yi wa kowa adalci.

Advertisement

Sakamakon wannan hukuncin da za a yanke a ranar Laraba, tuni hukumar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta dauki matakai domin dakile duk wata tarzoma da kan iya barkewa bayan sanar da hukuncin kotu.

Wani labarin kuma Kwanaki 100: Kotun Zabe Ta Tsige ‘Yan Majalisar Wakilai 25, Sanatoci 5 Na APC, PDP, LP da NNPP

Advertisement

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

Advertisement

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending