Connect with us

News

Mece ce gaskiyar maganar mayar da tallafin man fetur a Najeriya?

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Bincike ya nuna cewa duk da iƙirarin da gwamnatin tarayya ta yi cewa ta janye tallafin mai, ta sake mayar da shi a fakaice a baya-bayan nan.

Advertisement

Rahotanni na cewa gwamnatin tarayyar ta kashe fiye da naira biliyan 160 a watan Agustan da ya wuce don tsayar da farashin litar man fetur a kan naira 620.

Rundunar yan sandan jahar Kani ta Sanya dokar hana fita ta tashon awa 24

Gwamnatin ta yi hakan ne duk da tashin da farashin ɗanyen mai ya yi a kasuwar duniya da kuma faɗuwar da darajar naira

Masana dai na zargin cewa gwamnati na biyan tallafin ne a boye ganin matsin da al’umma ke ciki.

Advertisement

Tsayawar da farashin man ya yi a wuri guda a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ke tashi a duniya ya sa wasu masana tallatin arziki suna ƙaulani game da gaskiyar janye tallafin mai da gwamnati ta yi, wanda shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar a watan Mayun da ya wuce, inda gwamnati ta ce daga lokacin an bari kasuwa ta yi halinta.

 

Wani abu da ya ƙara wa zargin cewa gwamnati ta sake mayar da taffin shi ne wasu rahotanni da ke bayyana alƙaluman kuɗaɗen da gwamnatin ta kashe a tsakanin nan don taka wa farashin man fetur ɗin birki.

Advertisement

A hirarsa da BBC Dakta Ahmed Adamu masanin tattalin arzikin man fetur a Jami’ar Nile da ke Abuja, ya ce biri ya yi kama da mutum dangane da zargin komawa ruwa da gwamnatin ta yi.

 

Masanin ya ce idan aka duba za a ga cewa duk wasu shika-shikai da za su sa a samu tashin farashi a gidajen mai a Najeriya sun tabbata amma kuma farashin bai ƙaru ba.

Advertisement

 

Ya ce ɗanyen mai a kasuwar duniya ya kai dala 90 a kan duk ganga, saboda haka dole kuɗin da Najeriya ke sayo mai da shi ya ƙaru.

 

Advertisement

Kuma kuɗin shigowa da shi ma zai ƙaru. Bayan haka kuma kullum darajar naira a kan dala faɗuwa take.

 

“To idan aka duba waɗannan duka za a ga cewa komai da dala ake yi saboda haka dole ne farashin man a gidajen mai ya tashi, to amma rashin tashin ya sa a fahimci cewa lalle gwamnati ce ta dawo da tallafin,” in ji shi.

Advertisement

 

Sai dai kamfanin man Najeriyar bai ce komai game da maganar dawo da tallafin ba.

 

Advertisement

Amma dillalan man, waɗanda bisa al’ada su ake biya a tsarin tallafin sun ce ba tallafi gwamnati take bayarwa ba.

 

Shugaban ƙungiyar Arewa Oil And Gas marketers Association, AROGMA, Alhaji Bashir Dan-mallam shi ne wanda ya ce tashin farashin dalar ba ya shafar kamfanin NNPCL da ke shigo da man Najeriya kai-tsaye, kamar yadda dillan man ke sayen dala a kasuwar bayan fage.

Advertisement

 

Saboda haka ya ce gwamnati haƙuri take yi da ƙaramar riba don tirke farashin man, domin man da ƙasar ke fitarwa waje da dala take sayarwa kuma ta sayo tatacce daga wajen da dala, saboda haka daga cikin wannan kuɗi ne da take samu take haƙuri da kaɗan.

 

Advertisement

Masani, Dakta Ahmed Adamu ya sheda wa BBC cewa bai yi mamakin waiwayen da gwamnati ta yi na komawa bayar da tallafin ba.

 

Ya ce gwamnatin tarayyar ta ci da zuci ne a baya, ta janye tallafin man fetur din ba tare da cika wasu shika-shikai ba da za su hana wannan kwan-gaba-kwan-bayan, musamman ɗaukar matakan da za su rage buƙatar dala da faɗuwar darajar naira.

Advertisement

 

A ƙarshen watan Yunin da ya wuce ne, ‘yan Najeriya da dama suka faɗa cikin fargabar ƙarin farashin man fetur, ganin tallafin da gwamnati ke bayarwa ya kawo karshe.

 

Advertisement

A lokacin ne aka fara raɗe-raɗin cewa farshin litar man fetur, daga naira ɗari shida da ɗoriya zai yi mummunan tashi zuwa fiye da duk yadda ake tsammani.

 

Wannan ya jefa ƴan ƙasar cikin fargaba ta tsadar rayuwa ganin yadda tun ma kafin a cire tallafin yawanci suna cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa to ina ga kuma idan an cire tallafin.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *