News
Rundunar yan sandan jahar Kani ta Sanya dokar hana fita ta tashon awa 24

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar yan sandan jihar Kano ta Sanya dokar hana fita ta tashon awa 24 domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
”haka kuma sanarwar tace Ya kamata al’ummar jihar kano su sani tuni mun baza jami’an tsaro a lungu da sakon na jihar kano domin tabbatar da cewa al’umma sun bi wannan doka ta hana fita tsahon awa 24″ .
Jaridar Inda Ranka ta rawaito Kwamishinan Yan Sanda na jihar kano CP Muhammad Usaini Gumal ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu.
Sanarwar tace dokar ta fara aiki daga karfe 6 na yammacin Laraba, 20 ga Satumba zuwa karfe 6 na yammacin Alhamis, 21 ga Satumba, 2023. Kuma za’a hukunta duk wanda aka samu ya karya wannan doka. .
“Daga karshe ina mika godiyata ga daukacin al’ummar jihar nan masu son zaman lafiya tare da kira gare su da su ci gaba da bin doka da oda domin yana da amfani ga duk wanda muka taru domin tabbatar da doka da oda a jihar”.